Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 11:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Ta wurin bangaskiya ne, sa'ad da aka haifi Musa, iyayensa suka ɓoye shi har wata uku, domin sun ga yaron kyakkyawa ne, ba su kuma ji tsoron umarnin sarki ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Ta wurin bangaskiya ne iyayen Musa suka ɓoye shi har wata uku bayan haihuwarsa, domin sun ga cewa shi ba kamar sauran yara ba ne, ba su kuwa ji tsoron umarnin sarki ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 11:23
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Fir'auna kuwa ya umarci dukan mutanensa ya ce, “Duk jaririn da aka haifa wa Ibraniyawa, sai ku jefa shi cikin Kogin Nilu, amma idan jaririya ce, ku bar ta da rai.”


“Sa'ad da kuke yi wa matan Ibraniyawa hidimarku ta ungozomai, in kuka gan su durƙushe, in jariri ne suka haifa, sai ku yi masa sanadin mutuwa, in kuma jaririya ce, ku bar ta da rai.”


Saboda haka, ma iya fitowa gabagaɗi, mu ce, “Ubangiji shi ne mataimakina, Ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”


Kada ku ji tsoron masu kisan mutum, amma ba sa iya kashe kurwarsa. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon hallaka kurwar da jikin duka a Gidan Wuta.


A lokacin nan ne aka haifi Musa, yaro kyakkyawan gaske. Sai aka rene shi wata uku a gidan ubansa.


Ubangiji ya ce, “Isra'ila, ku kima ne marasa ƙarfi kuma, Kada ku ji tsoro, zan taimake ku. Ni Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ni ne mai fansarku.


Ubangiji yana tare da ni, ba zan ji tsoro ba. Me mutane za su iya yi mini?


Sa'ad da Daniyel ya sani an sa hannu a dokar, sai ya tafi gidansa. Ya buɗe tagogin benensa waɗanda suke fuskantar Urushalima. Sau uku kowace rana yakan durƙusa ya yi addu'a, yana gode wa Allahnsa kamar yadda ya saba.


Ubangiji ya ce, “Ni ne wanda yake ƙarfafa ku. Don me za ku ji tsoron mutum mai mutuwa, Wanda bai fi ciyawa tsawon rai ba?


“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuka san abin da yake daidai, Ku da kuke riƙe da koyarwata a zuciyarku. Kada ku ji tsoro sa'ad da mutane suke yi muku ba'a da zagi.


Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.


Ga Allah nake dogara, ina yabon alkawarinsa, Gare shi na dogara, ba zan ji tsoro ba. Me mutum kawai zai yi mini?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ