“Da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin Haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ban ji daɗinku ba. Ba zan karɓi hadayun da kuke kawo mini ba,” in ji Ubangiji Mai Runduna.
An biya ni sarai, har fi. Bukatata ta biya, da na karɓi kyautar da kuka aiko mini ta hannun Abafaroditas, baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.
Ba ka bukatar baye-baye da hadayu, Ba ka so a miƙa maka hadayun ƙonawa Na dabbobi a bisa bagade ba, Ko baya-baye don a kawar da zunubai. A maimakon haka, ka ba ni kunnuwan da zan saurare ka.