Kada ku ji tsoron masu kisan mutum, amma ba sa iya kashe kurwarsa. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon hallaka kurwar da jikin duka a Gidan Wuta.
Amma zan gaya muku wanda za ku tsorata. Ku ji tsoron wannan da in ya kashe, yana da ikon jefawa a cikin Gidan Wuta. Hakika, ina gaya muku, shi za ku ji tsoro!
Jama'ar Sihiyona cike da zunubi suke, suna ta rawar jiki don tsoro. Suka ce, “Hukuncin Allah kamar wuta ce mai ci har abada. Akwai wani daga cikinmu da zai iya tsira daga irin wannan wuta?”
Lokaci zai yi in da zuciyar mutanen Masar za ta narke kamar mata. Za su yi rawar jiki da razana lokacin da suka ga Ubangiji Mai Runduna ya miƙa hannunsa don ya hukunta su.
To, ga shi, hannun Ubangiji na kanka, za ka makance, ba za ka ga rana ba har wani lokaci.” A nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe shi, ya yi ta neman wanda zai yi masa jagora.
Da yake muna tsoron Ubangiji, shi ya sa muke ƙoƙarin rinjayar mutane. Yadda muke kuwa, ai, sananne ne ga Allah, muna fata ku ma haka abin yake a lamirinku.