Amma na biyun, sai babban firist kaɗai yake shiga, shi ma kuwa sai sau ɗaya a shekara, sai kuma da jini wanda yakan miƙa saboda kansa, da kuma kurakuran jama'a.
Sau ɗaya a shekara Haruna zai yi kafara a bisa zankayensa. Zai yi kafara a bisansa da jinin hadaya don zunubi ta yin kafara. Za a riƙa yin wannan dukan zamananku, gama bagaden mai tsarki ne ga Ubangiji.”
Wannan zai zama dawwamammiyar farilla a gare su. Za a riƙa yin kafara domin jama'ar Isra'ila saboda zunubansu duka sau ɗaya a shekara. Sai Musa ya aikata kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.