Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 10:20 - Littafi Mai Tsarki

20 ta wurin sabuwar hanya, rayayyiya wadda ya buɗe mana ta labulen nan, wato jikinsa,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 ta wurin sabuwa, rayayyiyar hanya kuma wadda aka buɗe mana ta labulen nan, wato, jikinsa,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 10:20
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.


Ni ne ƙofar. Kowa ya shiga ta wurina zai sami ceto, ya kai ya kawo, ya kuma yi kiwo.


Bayan labule na biyu kuma, akwai sashin alfarwa da ake kira Wuri Mafi Tsarki.


Ta haka Ruhu Mai Tsarki yake yin ishara, cewa ba a buɗe hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin alfarwa tana nan a tsaye,


Begen nan kuwa da muke da shi, kamar anka yake ga rai, kafaffe, tabbatacce, shi ne kuma yake shiga har can ciki bayan labulen,


Don haka Yesu ya sāke ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.


Ta haka za ku san Ruhun Allah, wato, duk ruhun da ya bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana ne da jiki, shi ne na Allah.


Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah. An kashe shi a jiki, amma an rayar da shi a ruhu.


Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai, An bayyana shi da jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, Mala'iku sun gan shi, An yi wa al'ummai wa'azinsa, An gaskata da shi a duniya, An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.


Hasken rana ya dushe. Labulen da yake cikin Haikali ya tsage gida biyu.


Sa'an nan labulen da yake cikin Haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa.


Sai labulen da yake cikin Haikalin ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta yi girgiza, duwatsu kuma suka tsattsage.


Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan'uwanka Haruna kada ya riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule ko yaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada ya mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin.


Gama masu ruɗi da yawa sun fito duniya, waɗanda ba sa bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana da jiki, irin wannan shi ne mai ruɗi, magabcin Almasihu.


Har ya soke Shari'ar nan mai umarni da dokoki, ta wurin ba da jikinsa, domin ta gare shi yă halicci sabon mutum guda daga mutanen nan biyu, ta haka yă kawo salama,


Sai dai ba zai kusaci labulen, ko ya tafi kusa da bagaden ba, domin yana da lahani, don kada ya ɓata wuraren yin sujada, gama ni ne Ubangiji, ni kuwa na tsarkake su.”


Sai kuma ya yanka bunsuru na yin hadaya don zunubin jama'ar ya shigar da jinin bayan labulen. Zai sa jinin kamar yadda ya yi da jinin bijimin, ya yayyafa shi a kan murfin, da gaban murfin.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ