18 To, a inda aka sami gafarar waɗannan, ba sauran wata hadaya domin kawar da zunubi.
18 In an gafarta zunubai, babu sauran bukatar miƙa hadaya.
In haka ne kuwa, ashe, ba sai a daina yin hadayar ba? Da an taɓa tsarkake masu ibadar nan sarai, ai, da ba su ƙara damuwa da zunubai ba.
Gama ta hadaya guda kawai ya kammala waɗanda aka tsarkake har abada.
sai kuma ya ƙara cewa, “Ba kuma zan ƙara tunawa da zunubansu da laifofinsu ba.”
Saboda haka, ya 'yan'uwa, tun da muke da amincewar shiga Wuri Mafi Tsarki, ta wurin jinin Yesu,