To, tun da yake Shari'a ishara ce kawai ta kyawawan abubuwan da suke a gaba, ba ainihin siffarsu ba, ashe, har abada ba za ta iya kammala waɗanda suke kusatar Allah ta wurin waɗannan hadayu ba, waɗanda ake yi a kai a kai kowace shekara.
balle fa jinin Almasihu wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah, ta wurin Madawwamin Ruhu, lalle zai tsarkake lamirinmu daga barin ibada marar tasiri, domin mu bauta wa Allah Rayayye.
da ya sa ni bawan Almasihu Yesu ga al'ummai, ina hidimar bisharar Allah, domin al'ummai su zama hadaya mai karɓuwa a gare shi, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, wato, su waɗanda aka keɓe a cikin Almasihu Yesu, tsarkaka kirayayyu, tare da dukan waɗanda a ko'ina suke addu'a, da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijinsu da namu duka.