Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ibraniyawa 1:1 - Littafi Mai Tsarki

1 A zamanin dā, Allah ya yi wa kakannin kakanninmu magana ta hanyoyi masu yawa iri iri, ta bakin annabawa,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ibraniyawa 1:1
35 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Bayan wannan zan zubo Ruhuna a kan jama'a duka, 'Ya'yanku mata da maza za su iyar da saƙona, Tsofaffinku kuwa za su yi mafarkai, Samarinku za su ga wahayi da yawa.


Sai ya fara ta kan littattafan Musa da na dukan annabawa, ya yi ta bayyana musu abubuwan da suka shafe shi a dukan Littattafai.


To, da yake shi annabi ne, ya kuma san Allah ya rantse masa, cewa zai ɗora wani daga cikin zuriya tasa kan kursiyinsa,


Ya cika faɗarsa ga kakanninmu, Ga Ibrahim da zuriyarsa, har abada.”


Mu ma mun kawo muku albishir, cewa, alkawarin nan da Allah ya yi wa kakanninmu,


Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”


In kuwa maganar nan da aka faɗa ta bakin mala'iku ta zama tabbatacciya, har kowane keta umarni da rashin biyayya, suka gamu da sakamakonsu wanda ya kamace su,


Domin nuna jinƙai ne ga kakanninmu, Ya tuna da alkawarinsa mai tsarkin nan.


Da suka sa masa rana, sai suka zo masaukinsa, su da yawa. Sa'an nan ya yi ta yi musu bayani, yana ta shaidar musu Mulkin Allah, tun daga safe har magariba, yana ƙoƙarin rinjayarsu a kan Yesu, ta hanyar Attaurar Musa da littattafan annabawa.


Mun dai sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan ba mu san ta inda ya fito ba.”


Musa ya bar muku kaciya, (ba ko shi ya fara ba, tun kakannin kakanni ne), ga shi kuma, kukan yi wa mutum kaciya ko a ran Asabar ma.


Ya kuma ce musu, “Wannan ita ce maganata da na gaya muku tun muna tare, cewa lalle ne a cika duk abin da yake rubuce game da ni a Attaura ta Musa, da littattafan annabawa, da kuma Zabura.”


Sai Ubangiji ya ce, “Numfashina ba zai zauna cikin mutum har abada ba, gama shi mai mutuwa ne. Nan gaba kwanakinsa ba zai ɗara shekara ɗari da ashirin ba.”


Sa'ad da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku cikin dukan gaskiya, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai faɗa, zai kuma sanar da ku al'amuran da za su auku.


wanda lalle ne ya zauna a Sama, har kafin lokacin nan na sabunta dukkan abubuwa da Allah ya faɗa tun zamanin dā ta bakin annabawansa tsarkaka.


to, ta ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji kansa, shi ne ya fara sanar da shi, waɗanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi,


To, shi Musa mai aminci ne ga dukkan jama'ar Allah a kan shi bara ne, saboda shaida a kan al'amuran da za a yi maganarsu a nan gaba,


Da dai a ce Joshuwa ya kai su cikin inuwar Allah, da Allah bai yi maganar wata rana nan gaba ba,


Haka kuma, Almasihu, ba shi ya ɗaukaka kansa ya zama Babban Firist ba, sai dai wannan ne ya sa shi, wanda ya ce da shi, “Kai Ɗana ne, Ni Ubanka ne yau.”


Don bayan Musa ya sanar da kowane umarnin Shari'a ga dukan jama'a, sai ya ɗebi jinin 'yan maruƙa da na awaki, tare da ruwa, da jan ulu, da kuma ganyen izob, ya yayyafa wa Littafin kansa, da kuma duk jama'a,


Domin ta gare ta ne shugabannin dā suka sami yardar Allah.


wanda a kansa aka yi faɗi cewa, “Ta wurin Ishaku ne za a lasafta zuriyarka.”


Ku kula fa, kada ku ƙi mai maganar nan. Domin in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi ma daga Sama?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ