Me za ku yi sa'ad Allah zai hukunta ku? Me za ku yi kuma sa'ad da ya kawo muku masifa daga wata ƙasa mai nisa? Ina za ku sheƙa neman taimako? A ina kuma za ku ɓoye dukiyarku?
Ya ku firistoci masu miƙa hadayu a bagaden Ubangiji, Ku sa tufafin makoki, ku yi kuka! Ku shiga Haikali, ku kwana, Kuna saye da tufafin makoki, Gama ba hatsi ko ruwan inabi da za a yi hadaya da su, A cikin Haikalin Allahnku.