Hosiya 9:4 - Littafi Mai Tsarki4 Ba za su yi wa Ubangiji hadaya ta sha ba. Ba za su faranta zuciyarsa da sadakoki ba. Abincinsu zai zama irin na masu makoki. Duk wanda ya ci shi zai haramta. Gama abincinsu zai yi musu maganin yunwa ne kawai, Ba za su kai shi Haikalin Ubangiji ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 Ba za su zuba hadayun ruwan inabi ga Ubangiji ba, ba kuwa hadayunsu za su gamshe shi ba. Irin hadayun nan za su zama musu kamar burodin masu makoki; duk wanda ya ci su zai ƙazantu. Wannan abincin zai zama na kansu ne; ba zai zo cikin haikalin Ubangiji ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu'a ga gumaka. Suna jin daɗin al'amuran banƙyama a lokacin yin sujada.