Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Hosiya 9:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Ubangiji ya ce, “Na iske Isra'ila a jeji kamar inabi, Na ga kakanninku kamar nunan fari na 'ya'yan ɓaure, Amma da suka zo Ba'al-feyor, sai suka keɓe kansu ga Ba'al. Suka zama abin ƙyama kamar abin da suke ƙauna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 “Sa’ad da na sami Isra’ila, ya zama kamar samun inabi a hamada; sa’ad da na ga kakanninku, ya zama kamar ganin ’ya’yan itace na farko a itacen ɓaure. Amma sa’ad da suka zo Ba’al-Feyor, suka keɓe kansu wa gumaka bankunya sai suka zama abubuwan banƙyama kamar abubuwan da suke ƙauna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Hosiya 9:10
32 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba zan hukunta 'ya'yanku mata sa'ad da suka yi karuwanci ba, Ko kuwa surukanku mata sa'ad da suka yi zina ba, Gama mazan da kansu sukan shiga wurin karuwai. Sukan miƙa sadaka tare da karuwai a Haikali, Mutane marasa fahimi za su lalace.


Gama yawan gumakansu sun kai yawan biranensu. Yawan bagadan da suke da su kuma sun kai yawan titunan Urushalima, abin kunya, bagadan ƙona wa Ba'al turare ne.’


Tawa ta ƙare, gama na zama kamar lokacin da aka gama tattara amfanin gona, Kamar lokacin da aka gama kalar 'ya'yan inabi, Ba nonon inabi da za a tsinka, a ci, Ba kuma 'ya'yan ɓaure da suka harba wanda raina yake so.


Can zan ba ta gonar inabi, In mai da kwarin Akor, wato wahala, ƙofar bege. A can za ta amsa mini kamar a kwanakin ƙuruciyarta, Kamar lokacin da ta fito daga ƙasar Masar.


Amma suka tayar mini, ba su ji ni ba, ba su yi watsi da abubuwan banƙyama da suke jin daɗinsu ba, ba su rabu da gumakan Masarawa ba. Sai na ce zan zubo musu da hasalata, in aukar musu da fushina a ƙasar Masar.


Ku miƙa abincinku hadaya ta godiya. Ku yi ta yin fariya da hadayarku ta yardar rai! Gama irin abin da kuke jin daɗin yi ke nan.”


“A lokacin da Isra'ila yake yaro, na ƙaunace shi, Daga cikin Masar na kirawo ɗana.


Haka Ubangiji ya ce, “Jama'ar da suka tsere wa takobi, Sun sami alheri a cikin jeji, A sa'ad da Isra'ila suka nemi hutawa.”


Annabawa sun yi annabcin ƙarya, Firistoci kuma sun yi mulki da ikon kansu, Mutanena kuwa suna so haka! Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me za ku yi?”


Darajan nan mai dushewa ta shugabanni masu girmankai za ta shuɗe kamar 'ya'yan ɓaure, nunan fari, da aka tsinke aka cinye nan da nan da nunarsu.


Saboda haka na bar su su yi ta kangarewarsu, Su aikata duk irin abin da suka ga dama.


Da yake abu ne mai sauƙi a gare shi ya bi hanyar zunuban Yerobowam ɗan Nebat, sai ya auro Yezebel 'yar Etba'al, Sarkin Sidon, ya kuma bauta wa gunkin nan Ba'al, ya yi masa sujada.


A ranar nan aka laƙaba wa Gidiyon suna Yerubba'al, wato “Bari gunki Ba'al ya yi hamayya don kansa, domin an farfashe bagadensa.”


Suka miƙa hadayu ga aljannun da ba Allah ba, Ga gumakan da ba su sani ba, Sababbin allolin da aka shigo da su daga baya, Waɗanda kakanninku ba su ji tsoronsu ba.


“Ya same shi daga cikin hamada, A jeji marar amfani, inda namomi suke kuka. Ya kewaye shi, ya lura da shi, Ya kiyaye shi kamar ƙwayar idonsa.


Idanunku sun ga abin da Ubangiji ya yi a Ba'al-feyor, yadda Ubangiji Allahnku ya hallaka dukan mutane daga cikinku da suka bauta wa Ba'al-feyor.


Tuntu zai zama musu abin dubawa don su riƙa tunawa da dukan umarnan Ubangiji su aikata su, don kada su bi son zuciyarsu, da sha'awar idanunsu yadda suka taɓa yi.


To, wace fa'ida kuka samu a lokacin nan, a game da aikin da kuke jin kunya a yanzu? Lalle ƙarshen irin wannan aiki mutuwa ne.


Ka sa waɗanda suka yi su, Da dukan masu dogara gare su, Su zama kamar gumakan da suka yi!


“Amma yin sujada ga gunkin nan Ba'al ya cinye mana amfanin wahalar da kakanninmu suka sha tun muna yara, wato na garkunan tumakinsu, da na awakinsu, da na shanunsu, da 'ya'yansu mata da maza.


A ɗaya kwandon akwai ɓaure masu kyau, kamar nunan fari. A ɗayan kuwa marasa kyau ne, ba mai iya cinsu.


Su taron mashaya ne kawai, Karuwai ne kuma. Suna ƙaunar abin kunya.


Nunan fari na dukan amfanin gonarsu wanda suke kawowa ga Ubangiji, zai zama naka. Duk wanda yake da tsarki a gidanka zai iya cinsa.


Suka ƙona turare a kan wuraren tsafi na kan tuddai kamar yadda al'ummar da Ubangiji ya kora daga gabansu suka yi. Suka aikata mugayen abubuwa, suka su Ubangiji ya yi fushi.


Wane ne wannan da yake fitowa daga cikin jeji, Kamar tunnuƙewar hayaƙi cike da kayan ƙanshi iri iri na fatake?


Bari mu kwanta mu sha kunyarmu, bari kuma rashin kirkinmu ya rufe mu. Gama mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi mu da kakanninmu, tun daga ƙuruciyarmu har zuwa yau, ba mu yi biyayya ga maganar Ubangiji Allahnmu ba.”


Ni ne wanda ya san ku a cikin jeji, A ƙasar da take da ƙarancin ruwan sama.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ