Ubangiji ya ce, “Mutanen Edom sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun farauci 'yan'uwansu, Isra'ilawa, Suka ƙi su nuna musu jinƙai. Ba su yarda su huce daga fushinsu ba.
“Ubangiji zai sa abokan gabanku su rinjaye ku cikin yaƙi. Ta hanya guda za ku auka musu, amma ta hanyoyi bakwai za ku gudu daga gabansu. Za ku zama abin ƙi ga dukan mulkokin duniya.
“Amma ga waɗanda suka ragu, zan sa fargaba a zuciyarsu sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu. Ko motsin ganye kawai ma zai razanar da su su sheƙa a guje kamar waɗanda ake fafara da takobi, ga shi kuwa, ba mai korarsu, za su kuwa fāɗi.
“Suna naɗa sarakuna, amma ba da iznina ba. Suna naɗa shugabanni amma ba da yardata ba. Suna ƙera gumaka da azurfarsu da zinariyarsu, Wannan kuwa zai zama sanadin halakarsu.