In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe ƙofa, kun kuma fara tsayawa daga waje, kuna ƙwanƙwasa ƙofar, kuna cewa, ‘Ya Ubangiji, buɗe mana,’ sai ya amsa muku ya ce, ‘Ku kam, ban san daga inda kuke ba.’
Shari'ar shugabannin ƙasar ta cin hanci ce. Firistocinta suna koyarwa don neman riba, Haka kuma annabawa suna annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna dogara ga Ubangiji, suna cewa, “Ai, Ubangiji yana tsakiyarmu, Ba masifar da za ta same mu.”