Idan akwai laifi a Gileyad, Hakika za su zama wofi. A Gilgal ana sadaka da bijimai, Bagadansu za su zama kamar tsibin duwatsu A gyaffan kunyoyin gona.”
“Ku ji wannan, ya ku firistoci! Ku saurara, ya mutanen Isra'ila! Ku kasa kunne, ya gidan sarki! Gama za a yi muku hukunci, Domin kun zama tarko a Mizfa, Da ragar da aka shimfiɗa a bisa Tabor.
Amma ina kama da lafiyayyen ɗan rago, Wanda aka ja zuwa mayanka, Ashe, ni suke ƙulla wa munafuncin! Ni kuwa ban sani ba, da suke cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da 'ya'yansa. Bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, Har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.”
“Ka kuma san abin da Yowab ɗan Zeruya ya yi mini, yadda ya kashe shugabannin sojoji na Isra'ila su biyu, wato Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya zubar da jinin yaƙi a lokacin salama. Ya sa jinin yaƙi a kan ɗamararsa wadda take gindinsa, da kuma kan takalmansa da yake ƙafafunsa.
Sa'ad da suke a babban dutsen Gibeyon, Amasa ya zo ya tarye su. A lokacin nan Yowab yana saye da rigar yaƙi, ya sha ɗamara, yana kuma rataye da takobi a ɗamararsa. Da ya gabato, sai takobin ya faɗi.
Sa'ad da Abner ya komo Hebron, sai Yowab ya raɓa da shi wajen ƙofar garin kamar zai gana da shi, sai ya soke shi a ruwan ciki, ya fāɗi ya mutu, saboda alhakin jinin ɗan'uwansa, Asahel.
Daga cikin kabilar Gad aka ba su birane huɗu, su ne Ramot ta Gileyad da wuraren kiwo nata, wannan birnin mafaka ne domin wanda ya yi kisankai, da Mahanayim da wuraren kiwo nata, da Heshbon da wuraren kiwo nata, da Yazar da wuraren kiwo nata.