Ko da yake Isra'ila tana bunƙasa kamar ciyayi, Iskar gabas, wato iskar da za ta zo daga jeji, Za ta busar da maɓuɓɓugarsu da idon ruwansu, Za ta lalatar da abubuwa masu amfani da yake cikin taskarsu.
Ifraimu tana kiwon iska, Tana ta bin iskar gabas dukan yini. Tana riɓaɓɓanya ƙarya da kamakarya. Tana ƙulla yarjejeniya da Assuriya, Tana kai mai a Masar.”
Ya Ubangiji, begen Isra'ila, Duk waɗanda suka rabu da kai, za su sha kunya. Waɗanda suka ba ka baya a duniya za a rubuta su Domin sun rabu da Ubangiji, maɓuɓɓugar ruwan rai.