Marar gaskiya yă yi ta rashin gaskiyarsa, fajiri kuwa yă yi ta fajircinsa, adali kuwa yă yi ta aikata adalcinsa, wanda yake tsattsarka kuwa ya yi ta zamansa na tsarki.”
Har yanzu suna ta ƙara yin zunubi, Suna yi wa kansu gumaka na zubi, Da gwaninta sukan yi gumaka da azurfarsu, Dukansu aikin hannu ne. Sukan ce, “Ku miƙa wa waɗannan hadayu!” Mutane sukan sumbaci siffofin maruƙa.
Ifraimu tana kiwon iska, Tana ta bin iskar gabas dukan yini. Tana riɓaɓɓanya ƙarya da kamakarya. Tana ƙulla yarjejeniya da Assuriya, Tana kai mai a Masar.”