Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Hosiya 4:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Mutanen Isra'ila masu taurinkai ne kamar alfadari. Ta yaya Ubangiji zai yi kiwonsu Kamar 'ya'yan tumaki a makiyaya mai fāɗi?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Isra’ilawa masu taurinkai ne, kamar karsana mai taurinkai. Yaya Ubangiji zai iya kiwonsu kamar tumaki a makiyaya mai ɗanyar ciyawa?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Hosiya 4:16
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Amma suka ƙi ji, suka ba da baya, suka toshe kunnuwansu don kada su ji.


Mutanena sun himmantu su rabu da ni, Ko da yake an kira su ga Ubangiji, Ba wanda ya girmama shi.


Irmiya ya ce, “Ko da yake zunubanmu su ne shaidunmu, Ya Ubangiji, ka yi taimako saboda sunanka! Gama kāsawarmu ta yi yawa, Domin mun yi maka zunubi.


Me ya sa, mutanen nan na Urushalima suke ratsewa, suke komawa baya kullayaumin? Sun riƙe ƙarya kan-kan Sun ƙi komowa.


Amma ba su yi biyayya ba, ba su kuma kula ba. Sai suka bi shawarar kansu da ta tattaurar muguwar zuciyarsu. Suka koma baya maimakon su yi gaba.


Domin haka zaki daga kurmi zai kashe su, Kyarkeci kuma daga hamada zai hallaka su. Damisa tana yi wa biranensu kwanto, Duk wanda ya fita daga cikinsu sai a yayyage shi, Domin laifofinsu sun yi yawa, Karkacewarsu babba ce.


Ubangiji kuma ya faɗa mini, ko da yake Isra'ila ta bar binsa, duk da haka ta nuna laifinta bai kai na Yahuza marar aminci ba.


Yahuza kuwa ta ga dukan karuwancin da marar amincin nan, Isra'ila ta yi, na sake ta, na ba ta takardar sarki. Amma duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza, ba ta ji tsoro ba, amma ita ma ta tafi ta yi karuwanci.


A zamanin sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da take yi, ita marar amincin nan, wato Isra'ila? Yadda a kowane tudu mai tsayi, da a gindin kowane itace mai duhuwa, a wurare ne ta yi karuwancinta.


Zai dunƙule ka kamar ƙwallo ya jefa ka a cikin ƙasar da ta fi girma. A can za ka mutu a kusa da karusan da kake fāriya da su. Abin kunya kake a gidan maigidanka!


A cikin kangwayen birnin, raguna za su ci ciyawa, a nan ne kuma awaki za su sami wurin kiwo.


Zan sa a kawo muku yaƙi a warwatsa ku a baƙin ƙasashe, ƙasarku za ta zama kufai, biranenku kuwa za su lalace.


Kada su zama kamar kakanninsu, Jama'ar 'yan tawaye marasa biyayya. Ba su taɓa dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya ba, Ba su kuwa yi masa aminci ba.


Duk lokacin da kuka shuka amfanin gonakinku, Ubangiji zai aiko da ruwan sama ya sa su girma, zai ba ku kaka mai albarka, shanunku kuma za su sami makiyaya wadatacciya.


“Na ji Ifraimu yana baƙin ciki, yana cewa, ‘Ka hore ni, na kuwa horu, Kamar ɗan maraƙin da ba shi da horo, Ka komo da ni don in zama kamar yadda nake a dā, Gama kai ne Ubangiji Allahna.


“Ifraimu horarriyar karsana ce, Wadda yake jin daɗin yin sussuka, Amma na sa wa kyakkyawan wuyanta karkiya, Na sa Yahuza ta ja garmar noma, Yakubu kuwa za ta ja garmar bajiya.


Takobi zai ragargaje biranensu, Zai lalatar da sandunan ƙarafan ƙofofinsu, Zai cinye su domin muguwar shawararsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ