Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Hosiya 2:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Don haka zan hana mata hatsi a kakarsa, Da ruwan inabi a kakarsa, da kuma ulu da lilin Waɗanda suka zama abin rufe tsiraicinta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 “Saboda haka zan ƙwace hatsina sa’ad da ya nuna, da sabon ruwan inabina sa’ad da ya ƙosa. Zan karɓe ulu nawa da lilina, da take niyya ta rufe tsiraicinta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Hosiya 2:9
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan za ku ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, da tsakanin mutumin da yake bauta mini da wanda ba ya bauta mini.”


Edomawa, wato zuriyar Isuwa, sun ce, “An rurrushe garuruwanmu, amma za su sāke gina su.” Sa'an nan Ubangiji zai amsa, ya ce, “To, su gina mana, ai, zan sāke rurrushe su. Mutane za su ce da ƙasarsu, ‘Ƙasar mugaye, da al'ummar da Ubangiji yake fushi da ita har abada.’ ”


In ba haka ba, sai in yi mata tsiraici, In bar ta kamar ran da aka haife ta. In maishe ta kamar jeji, In bar ta kamar busasshiyar ƙasa, In kashe ta da ƙishi.


Za a washe dukiyarsu, Za a kuwa rurrushe gidajensu, Ko da yake sun gina gidaje, ba za su zauna a ciki ba, Ko da yake sun dasa inabi, ba za su sha ruwansa ba.”


Wa ya sani ko Ubangiji Allahnmu zai sāke nufinsa, Ya sa mana albarka, Har mu miƙa masa hadaya ta gari da ta sha?


Masussuka da wurin matsa ruwan inabi ba za su ciyar da su ba. Sabon ruwan inabi kuma ba zai ishe su ba.


Gama sun shuka iska Don haka zu su girbe guguwa. Hatsin da yake tsaye ba shi da zangarniya, Ba zai yi tsaba ba. Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci,


Sarkin arewa kuwa zai tara babbar rundunar soja fiye da ta dā. Bayan waɗansu shekaru kuwa zai kama hanya da babbar rundunar soja, da kayan faɗa masu yawan gaske.


Za su tsiraita ki, su kuma kwashe lu'ulu'anki.


Zan bashe ki a hannun kwartayenki, za su kuwa rushe ɗakunan tsafinki, su tuɓe tufafinki, su kwashe murjaninki, su bar ki tsirara tik.


“Domin haka na miƙa hannuna gāba da ke, na rage rabonki, na ba da ke ga abokin gābanki masu haɗama, 'yan matan Filistiyawa waɗanda suka ji kunya saboda halinki na lalata.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ