Hosiya 2:8 - Littafi Mai Tsarki8 “Amma ba ta sani ni nake ba ta hatsi, da ruwan inabi, da mai, Da azurfa, da zinariya da yawa Waɗanda suka bauta wa gunkin nan Ba'al da su ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Ba ta yarda cewa ni ne wanda ya ba ta hatsi, sabon ruwan inabi da mai ba, wanda ya jibge mata azurfa da zinariya, waɗanda suka yi amfani wa Ba’al ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.