Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Hosiya 2:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Gama uwarsu ta yi karuwanci. Ita wadda ta haife su ta yi abin kunya. Gama ta ce, ‘Zan bi samarina Waɗanda suke ba ni ci da sha, Da ulu, da lilin, da mai, da ruwan inabi.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Mahaifiyarsu ta yi rashin aminci ta kuma ɗauki cikinsu ta wurin yi abin kunya. Ta ce, ‘Zan bi kwartayena, waɗanda suke ba ni abinci da ruwa, ulu nawa da lilina, mai nawa da kuma abin sha na.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Hosiya 2:5
33 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka sāke tafiya, ka ƙaunaci karuwa wadda take tare da kwartonta. Ka ƙaunace ta kamar yadda ni Ubangiji nake ƙaunar mutanen Isra'ila, ko da yake suna bin gumaka, suna ƙaunar wainar zabibi da aka miƙa wa gumaka.”


“Amma ba ta sani ni nake ba ta hatsi, da ruwan inabi, da mai, Da azurfa, da zinariya da yawa Waɗanda suka bauta wa gunkin nan Ba'al da su ba.


Birnin da yake dā mai aminci ne, yanzu ya zama kamar karuwa! Dā adalai a can suke zaune, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai.


Ubangiji ya ce, “Na iske Isra'ila a jeji kamar inabi, Na ga kakanninku kamar nunan fari na 'ya'yan ɓaure, Amma da suka zo Ba'al-feyor, sai suka keɓe kansu ga Ba'al. Suka zama abin ƙyama kamar abin da suke ƙauna.


Gama sun haura zuwa Assuriya, Kamar jakin jeji da yake yawo shi kaɗai. Mutanen Ifraimu sun yi ijara da abokan tsafinsu.


Za ku yi tuntuɓe da rana, Annabi kuma zai yi tuntuɓe tare da kai da dare, Ni kuwa zan hallaka mahaifiyarku.


“Ku roƙi uwarku, Gama ita ba matata ba ce, Ni kuma ba mijinta ba ne. Ku roƙe ta ta daina karuwancinta, Ta rabu da masu rungumar mamanta.


Gama yawan gumakansu sun kai yawan biranensu. Yawan bagadan da suke da su kuma sun kai yawan titunan Urushalima, abin kunya, bagadan ƙona wa Ba'al turare ne.’


“Ya Isra'ila, tun da daɗewa, ka ƙi yarda Ubangiji ya mallake ka, Ka ƙi yin biyayya da ni, Ka kuwa ce, ‘Ba zan yi bauta ba.’ Amma ka yi karuwanci a kan kowane tudu, Da kowane ɗanyen itace.


Ubangiji ya ce, “Kuna tsammani na kori mutanena Kamar yadda mutum yakan saki mata tasa? To, in haka ne ina takardar kisan auren? Kuna tsammani na sayar da ku cikin bauta Kamar mutumin da ya sayar da 'ya'yansa? A'a, kun tafi bauta ne saboda da zunubanku, Aka tafi da ku saboda da laifofinku.


Shugabannin Filistiyawa kuwa suka taru domin su miƙa babbar hadaya ga allahnsu, Dagon. Suka raira waƙa, suka ce, “Allahnmu ya ba da Samson, maƙiyinmu a hannunmu!”


Sa'ad da Ubangiji ya fara yin magana da Yusha'u ya ce masa, “Tafi ka auro karuwa, ka haifi 'ya'yan karuwanci, gama ƙasar tana yin fasikanci sosai, wato ta bar bin Ubangiji.”


Ku ji faɗaka, ya ku mutanen Urushalima, Don kada a raba ni da ku, Don kada in maishe ku kufai, Ƙasar da ba mazauna ciki.”


Idan kun ce a zuciyarku, ‘Me ya sa waɗannan abubuwa suka same mu?’ Saboda yawan zunubanku ne, Shi ya sa an tone tsiraicinku, Aka wahalshe ku.


Game da haihuwarki kuwa, ran da aka haife ki, ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka da ruwa don a tsabtace ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba, ba a naɗe ki cikin tsummoki ba.


Domin haka, ya ke karuwa, ki ji maganar Ubangiji.


Zan bashe ki a hannun kwartayenki, za su kuwa rushe ɗakunan tsafinki, su tuɓe tufafinki, su kwashe murjaninki, su bar ki tsirara tik.


A ranan nan kyawawan 'yan mata da samari Za su faɗi saboda ƙishirwa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ