domin kada ku yi cuɗanya da sauran al'umman da take zaune tare da ku, kada ku ambaci sunayen gumakansu, ko ku rantse da su, ko ku bauta musu, ko ku sunkuya musu.
A wannan rana fa, ni Ubangiji Mai Runduna, zan shafe sunayen gumaka daga ƙasar, har da ba za a ƙara tunawa da su ba. Zan kuma kawar da annabawa da mugayen aljannu.
Musa da jama'ar Isra'ila suka raira wannan waƙa ga Ubangiji suka ce, “Zan raira waƙa ga Ubangiji, gama ya ci gawurtacciyar nasara, Dawakai da mahayansu ya jefar cikin bahar.
Suka tara tsibin duwatsu a kansu. Tsibin duwatsun kuwa yana nan har wa yau. Sa'an nan Ubangiji ya huce daga zafin fushinsa. Domin haka ana kiran wurin Kwarin Akor, wato azaba, har wa yau.
in tafi in yi shelar abin da Ubangiji ya ce a kunnen Urushalima, in ce, “Na tuna da amincinki a lokacin ƙuruciyarki, Da ƙaunarki kamar ta amarya da ango. Yadda kika bi ni a cikin jeji, da a ƙasar da ba a shuka ba.