Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Hosiya 14:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Duk wanda yake da hikima, bari ya fahimci abubuwan nan. Duk wanda yake da ganewa, bari ya san abubuwan nan, Gama hanyoyin Ubangiji masu gaskiya ne, Masu adalci kuwa za su yi tafiya a cikinsu, Amma masu zunubi za su yi tuntuɓe a kansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Wane ne yake da hikima? Zai gane waɗannan abubuwa. Hanyoyin Ubangiji daidai ne; masu adalci sukan yi tafiya a kansu, amma ’yan tawaye sukan yi tuntuɓe a kansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Hosiya 14:9
46 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji yana kiyaye marasa laifi, amma yakan hallaka masu mugunta.


Da ma a ce masu hikima Za su yi tunani a kan waɗannan abubuwa, Da ma kuma su yarda Da madawwamiyar ƙaunar Ubangiji.


Na Allah yakan saurari Maganar Allah. Abin da ya sa ba kwa sauraronta ke nan, don ku ba na Allah ba ne.”


Mutane da yawa za su tsarkake kansu, su zama masu tsabta tsab tsab, amma mugaye ba za su gane ba, za su yi ta muguntarsu, amma masu hikima za su gane.


Ubangiji wanda yake cikinsa mai adalci ne, Ba ya kuskure. Yakan nuna adalcinsa kowace safiya, Kowace safiya kuwa bai taɓa fāsawa ba. Amma mugu bai san kunya ba.


Wa yake da isasshiyar hikimar da zai fahimci wannan? Wa Ubangiji ya faɗa masa don ya sanar? Me ya sa ƙasar ta lalace ta zama kufai, har ba wanda yake iya ratsa ta, kamar hamada?


“Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne, Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne. Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi, Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.


Sai Bilatus ya ce masa, “Wato ashe, sarki ne kai?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa, ni sarki ne. Domin haka musamman aka haife ni, don haka kuma musamman na shigo duniya, domin in shaidi gaskiya. Kowane mai ƙaunar gaskiya kuwa yakan saurari muryata.”


Ka sa hanyar mutanen kirki ta yi sumul, Hanyar da suke bi ta yi bai ɗaya,


Saboda haka ina bin dukan koyarwarka, Ina kuwa ƙin dukan mugayen al'amura.


Na sani ka'idodinka na adalci ne, ya Ubangiji, Ka hore ni, domin kai mai aminci ne.


Wannan ya yi nesa da kai, da ka aikata irin haka, wato da za ka aza mai adalci daidai yake da mugu! Wannan ya yi nesa da kai! Mahukuncin dukan duniya ba zai yi adalci ba?”


Domin haka Shari'a da kanta mai tsarki ce, umarnin kuma mai tsarki ne, daidai ne, nagari ne.


Da ba domin na yi ayyuka a cikinsu da ba wanda ya taɓa yi sai ni ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gani, sun kuma ƙi mu, ni da Ubana duka.


Yesu ya ce, “Na shigo duniyan nan ne don rarrabewa, domin waɗanda ba sa gani su gani, waɗanda suke gani kuma su makance.”


Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”


Sai Saminu ya sa musu albarka, ya ce wa Maryamu uwar Yesu, “Kin ga wannan yaro, shi aka sa ya zama sanadin faɗuwar waɗansu, tashin waɗansu kuma da yawa cikin Isra'ila, Zai kuma zama alama wadda ake kushenta,


Ga Ɗan Mutum ya zo, yana ci yana sha, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’ Duk da haka hikimar Allah, ta aikinta ne ake tabbatar da gaskiyarta.”


“Amma kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ku ji ya ku mutanen Isra'ila, hanyata ba daidai ba ce? Ashe, ba hanyarku ce ba daidai ba?


Amma zai ragargaza dukan wanda ya yi zunubi, ya tayar gāba da shi, zai kashe duk wanda ya rabu da shi.


Hanyar da adalai suke bi kamar fitowar rana ce, sai ta yi ta ƙara haske, har ta take tsaka.


Sukan yi ta ƙara jin ƙarfi a cikin tafiyarsu, Za su kuwa ga Allahn alloli a Sihiyona!


Masu murna ne waɗanda suka sami ƙarfinsu daga gare ka, Su waɗanda suka ƙosa su kai ziyara a Dutsen Sihiyona.


Har su ma da suke cewa su mutanen kirki ne Suna ƙara tabbatarwa ba su yi kuskure ba.


ya ce, “Kai babban maha'inci, munafiƙi, ɗan Iblis, magabcin adalci duka, ba za ka daina karkata miƙaƙƙun hanyoyin Ubangiji ba?


Suna raira waƙar da Musa bawan Allah ya yi, da kuma wadda ake yi wa Ɗan Ragon nan, suna cewa, “Ayyukanka manya ne, masu banmamaki, Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki! Hanyoyinka na adalci ne, na gaskiya ne kuma, Ya Sarkin al'ummai.


Mutum mai hikima, wanda ya isa mutum, akan san shi ta wurin haziƙancinsa, kamar yadda kalmominsa suke da daɗi, haka ma rinjayarsa take.


Ba za su ƙara dogara ga bagaden da suka yi da hannuwansu ba, ko kuwa su dogara ga ayyukan hannuwansu, ko keɓaɓɓun wuraren da suke wa gumaka sujada, ko bagadai don ƙona turare.


Sa'an nan za ku yi kira a gare ni, ku yi addu'a a wurina, zan kuwa ji ku.


Sa'ad da suka koma a ƙasar za su kawar da dukan abin da ya ƙazantar da ita, da dukan irin abar ƙyama da take cikinta.


Zan yayyafa muku tsabtataccen ruwa, za ku kuwa tsarkaka daga dukan ƙazantarku, da kuma daga dukan gumakanku.


“Zan sa jama'ar Yahuza ta yi ƙarfi, Zan ceci jama'ar Yusufu. Zan dawo da su domin ina jin tausayinsu. Za su zama kamar waɗanda ban taɓa ƙyale su ba, Gama ni Ubangiji Allahnsu ne, Zan amsa musu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ