Muguntarka za ta hore ka, Riddarka kuma za ta hukunta ka. Sa'an nan za ka sani, ka kuma gane, Ashe, mugun abu ne, mai ɗaci, a gare ka Ka rabu da Ubangiji Allahnka, Ba ka tsorona a zuciyarka. Ni Ubangiji, Allah Mai Runduna na faɗa.”
Ayyukansu na son zuciya za su zama shaida gāba da su. Suna ta aikata zunubi a fili, kamar yadda mutanen Saduma suka yi. Sun shiga uku, su ne kuwa suka jawo wa kansu.
Mai farin ciki ne kai, ya Isra'ila! Wane ne kamarku, mutanen da Ubangiji ya ceta? Ubangiji ne garkuwarku, Shi ne kuma takobinku mai daraja. Magabtanku za su yi muku fādanci, Amma ku za ku tattake masujadansu.”
Kuka kuma ce, ‘Mun gaji da wannan irin abu fa!’ Kuna hura mini hanci. Kukan kawo satacciyar dabba, ko gurguwa ko marar lafiya, ku yi mini hadaya da ita! Kuna tsammani zan karɓi wannan daga gare ku?
Gama ya miƙa hadaya ga gumakan Dimashƙu, ga waɗanda suka ci shi da yaƙi, ya ce, “Saboda gumakan sarakunan Suriya sun taimake su, ni ma zan miƙa musu hadaya don su taimake ni.” Amma suka zama masa dalilin lalacewa, shi da dukan Isra'ila.