Domin haka zaki daga kurmi zai kashe su, Kyarkeci kuma daga hamada zai hallaka su. Damisa tana yi wa biranensu kwanto, Duk wanda ya fita daga cikinsu sai a yayyage shi, Domin laifofinsu sun yi yawa, Karkacewarsu babba ce.
Amos ya ce, “Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona, Muryarsa za ta yi tsawa daga Urushalima. Da jin wannan, sai wuraren kiwo za su bushe, Ƙwanƙolin Dutsen Karmel, da yake kore zai yi yaushi.”
Ubangiji ya fita domin ya yi yaƙi kamar jarumi, Ya shirya, ya kuma ƙosa domin yaƙi. Ya yi gunzar yaƙi da tsawar yaƙi, Ya nuna ikonsa a kan abokan gābansa.
Dabbar da na gani kuwa kamar damisa take, ƙafafunta kamar na beyar, bakinta kuma kamar na zaki. Macijin kuwa ya ba ta ƙarfinsa, da kursiyinsa, da ikonsa mai girma.