Ubangiji ya bishe ku cikin babban jejin nan mai bantsoro, ƙasa mai macizai masu zafin dafi, da kunamai, da busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa. Ubangiji kuwa ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara.
Gama Ubangiji Allahnku ya sa albarka a kan dukan ayyukan hannuwanku. Ya kuma san tafiye-tafiyenku cikin babban jejin nan. Ubangiji Allahnku yana tare da ku a shekara arba'in ɗin nan, ba ku rasa kome ba.’
Amma a yanzu da kuka san Allah, ko ma dai a ce Allah ya san ku, ta yaya za ku sāke komawa a kan raunanan al'adu marasa biyan bukata, har kuna neman komawa ga bautarsu?
Ya Allah, kai ne Allahna, Ina sa zuciya gare ka. Duk niyyata ta nemanka ce, Raina yana ƙishinka, Kamar bussasshiyar ƙasa, Wadda ta zozaye, ba ta da ruwa.
Ba su kula da ni ba, Ko da yake na cece su daga ƙasar Masar. Na bi da su a cikin hamada, A ƙasa mai tuddai da kwazazzabai, Busasshiya mai yawan hatsari, Ba a bi ta cikinta, Ba wanda yake zama cikinta kuma.
in tafi in yi shelar abin da Ubangiji ya ce a kunnen Urushalima, in ce, “Na tuna da amincinki a lokacin ƙuruciyarki, Da ƙaunarki kamar ta amarya da ango. Yadda kika bi ni a cikin jeji, da a ƙasar da ba a shuka ba.
Ubangiji ya ce, “Na iske Isra'ila a jeji kamar inabi, Na ga kakanninku kamar nunan fari na 'ya'yan ɓaure, Amma da suka zo Ba'al-feyor, sai suka keɓe kansu ga Ba'al. Suka zama abin ƙyama kamar abin da suke ƙauna.