Hosiya 13:3 - Littafi Mai Tsarki3 Don haka za su zama kamar ƙāsashin da akan yi da safe, Ko kuwa kamar raɓa mai kakkaɓewa da wuri. Za su zama kamar ƙaiƙayi wanda ake shiƙarsa cikin iska a masussuka, Ko kuwa kamar hayaƙin da yake fita ta bututu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Saboda haka za su zama kamar hazon safiya, kamar raɓar safen da yakan kakkaɓe, kamar ƙaiƙayin da ake tankaɗe daga masussuka, kamar hayaƙin da yake fita daga taga. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan baƙin ƙarfen, da yumɓun, da tagullar, da azurfar, da zinariyar suka ragargaje gaba ɗaya, duka suka zama kamar ƙaiƙayi na masussuka da kaka. Iska kuwa ta kwashe su ta tafi da su, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma wannan dutse da ya buge mutum-mutumin ya girke, ya zama babban dutse ya cika duniya duka.