12 “An ƙunshe muguntar Ifraimu, Zunubinsa kuwa an ajiye shi a rumbu.
12 An yi ajiyar laifin Efraim, aka lissafta zunubansa.
Za ka soke zunubaina ka kawar da su, Za ka shafe dukan kurakuran da na taɓa yi.
Amma ga shi, saboda ƙeƙasasshiyar zuciyarka marar tuba, kana nema wa kanka fushin Allah a ranar fushi, sa'ad da za a bayyana hukuncin Allah macancani.
“Kukan ce Allah yakan hukunta yaro saboda zunuban mahaifinsa. A'a! Allah dai yakan hukunta wa masu zunubi. Ya kuma nuna ya yi haka saboda zunubansu ne.
Ko da za ka yi wanka da sabulun salo, Ka yi amfani da sabulu mai yawa, Duk da haka zan ga tabban zunubanka. Ni Ubangiji Allah na faɗa.