Ni ne Allahnku wanda yake cetonku daga dukan masifu da wahalai, amma ga shi yau, kun ƙi ni kuna roƙona in ba ku sarki. To, da kyau, yanzu fa sai ku kusato gaban Ubangiji kabila kabila da iyali iyali.’ ”
Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Har yaushe za ka yi ta ɓacin rai saboda Saul? Ga shi kuwa, na ƙi shi da zama Sarkin Isra'ila. Ka sami man zaitun ka ɗauka. Zan aike ka zuwa wurin Yesse mutumin Baitalami, gama na zaɓi ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza ya zama sarki.”
“Suna naɗa sarakuna, amma ba da iznina ba. Suna naɗa shugabanni amma ba da yardata ba. Suna ƙera gumaka da azurfarsu da zinariyarsu, Wannan kuwa zai zama sanadin halakarsu.