5 Ubangiji Allah Mai Runduna, Sunansa Ubangiji,
5 Ubangiji Allah Maɗaukaki, Ubangiji ne sunansa sananne!
Allah kuma ya sāke ce wa Musa, “Faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ubangiji Allah na kakanninku, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu ya aiko ni gare ku.’ Wannan shi ne sunana har abada. Da wannan suna za a tuna da ni a dukkan zamanai.
“Ni kaɗai ne Ubangiji Allahnka. Ba wani allahn da zai sami ɗaukakata, Ba zan bar gumaka su sami yabona ba.
Ya Ubangiji, kullayaumi mutane za su sani kai ne Allah, Dukan tsararraki za su tuna da kai.
Saboda haka Yakubu ya sa wa wurin suna Feniyel, yana cewa, “Gama na ga Allah fuska da fuska, duk da haka ban mutu ba.”
Yakubu ya farka daga barcinsa, ya ce, “Hakika, Ubangiji yana wurin nan, ni kuwa ban sani ba.”
Ku raira yabo ga Ubangiji, Ku amintattun jama'arsa! Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya aikata, Ku yi masa godiya!
Allah kuma ya sāke bayyana ga Yakubu a lokacin da ya komo daga Fadan-aram, ya sa masa albarka.