Hosiya 10:8 - Littafi Mai Tsarki8 Za a hallaka masujadan tuddai na Awen inda Isra'ila suke yin zunubi, Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma a bagadansu. Za su ce wa manyan duwatsu, “Ku rufe mu!” Su ce wa tuddai, “Ku faɗo bisa kanmu!” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Za a hallaka masujadai kan tudu na mugunta zunubin Isra’ila ne. Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma su rufe bagadansu. Sa’an nan za su ce wa duwatsu, “Ku rufe mu!” Ga tuddai kuma, “Ku fāɗo a kanmu!” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da aka gama duka, sai dukan Isra'ilawa da suka hallara, suka bi cikin biranen Yahuza, suka farfashe al'amudan, suka ragargaza Ashtarot, suka farfashe masujadai da bagadai duka da suke a Yahuza da Biliyaminu, da na Ifraimu da Manassa har suka hallakar da su duka. Sa'an nan dukan jama'ar Isra'ila suka koma garuruwansu, ko wanne zuwa mahallinsa.