Hosiya 10:4 - Littafi Mai Tsarki4 Surutai kawai suke yi, Suna yin alkawaran ƙarya, Don haka hukunci zai zaburo kamar muguwar ciyawa mai dafi a kunyoyin gona. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 Sun yi alkawura masu yawa, suka yi rantsuwar ƙarya da kuma yarjejjeniyoyi; saboda haka ƙararraki suka taso kamar ciyayi masu dafi da aka nome a gona. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Isra'ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna, Jama'ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa. Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau, Amma a maimakon haka sai suka zama masu kisankai! Ya zaci za su aikata abin da yake daidai, Amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci!