8 Sa'ad da ta yaye Ba-jinƙai, ta sāke ɗaukar ciki, ta haifi ɗa namiji.
8 Bayan ta yaye Lo-Ruhama, sai Gomer ta sāke haifi wani ɗa namiji.
Gomer ta kuma ɗauki ciki, ta haifi 'ya mace. Ubangiji kuma ya ce wa Yusha'u, “Ka raɗa mata suna Bajinƙai, gama ba zan ƙara yi wa jama'ar Isra'ila jinƙai ba, har da zan gafarta mata.
Amma zan yi wa mutanen Yahuza jinƙai. Ni kaina zan cece su ba da baka ba, ba kuwa da takobi, ko da yaƙi, ka da dawakai, ko da sojojin dawakai ba.”
Ubangiji kuma ya ce masa, “Ka raɗa masa suna, Ba-mutanena-ba-ne, gama ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne.
Yaron ya yi girma, aka yaye shi, Ibrahim kuwa ya yi babban biki a ranar da aka yaye Ishaku.