Sai mutanen kabilan Yusufu suka ce, “Ƙasar tuddai ba ta ishe mu ba, ga kuma Kan'aniyawa da suke zaune a filin, da waɗanda suke a Bet-sheyan da ƙauyukanta, da waɗanda suke cikin Kwarin Yezreyel suna da karusan ƙarfe.”
“A waccan rana zan yi alkawari Da namomin jeji, da tsuntsaye, Da abubuwa masu rarrafe saboda Isra'ila. Zan kuma kakkarya baka da takobi, In kuma sa yaƙi ya ƙare a ƙasar, Sa'an nan za su yi zamansu lami lafiya.
A zamanin Feka Sarkin Isra'ila, sai Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya, ya zo ya ci Iyon, da Abel-bet-ma'aka, da Yanowa, da Kedesh, da Hazor, da Gileyad, da Galili, da dukan ƙasar Naftali. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa bauta a Assuriya.