Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Haggai 2:6 - Littafi Mai Tsarki

6 “Ni Ubangiji Mai Runduna, ina cewa ba da jimawa ba, zan girgiza sammai, da duniya, da teku, da sandararriya ƙasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ba da jimawa ba zan sāke girgiza sammai da kuma ƙasa, teku da busasshiyar ƙasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Haggai 2:6
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saura kaɗan in gama hukuncin da nake yi muku, sa'an nan in hallaka su.


Zan nuna abubuwan al'ajabi a sararin sama, Da mu'ujizai a nan ƙasa, Wato jini, da wuta, da kuma, hauhawan hayaƙi.


Ubangiji yana magana da ƙarfi daga Sihiyona, Yana tsawa daga Urushalima, Sammai da duniya sun girgiza. Amma Ubangiji shi ne mafakar jama'arsa, Shi ne kagarar mutanen Isra'ila.


Kamar yadda karin maganar ta ce, kafin a jima kurmi zai zama gona, gona kuma za ta zama kurmi.


“Sauran lokaci kaɗan, Mai zuwan nan zai zo, ba kuwa zai yi jinkiri ba.


Kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da bisashe, da dukan masu rarrafe, da dukan mutanen da suke duniya, za su yi makyarkyata a gabana. Za a jefar da duwatsu ƙasa, tsaunuka za su fādi, kowane bango zai rushe.


Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila na ce, “Mutanen Babila sun zama kamar daɓen masussuka A lokacin da ake sussuka, Ba kuwa da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.”


Za a murtsuke rana, da wata, da taurari su zama ƙura. Sararin sama zai shuɗe kamar yadda ake naɗe littafi, taurari kuma su faɗo kamar yadda ganyaye suke karkaɗewa daga itacen inabi ko na ɓaure.


A ɗan ƙanƙanen lokaci mugaye za su shuɗe, Za ka neme su, amma ba za a same su ba,


Mutanen dukkan jama'a, da kabila, da harshe, da al'umma za su riƙa kallon gawawwakinsu, har kwana uku da rabi, su kuwa ƙi yarda a binne su.


Allah yakan aiko da girgizar ƙasa, ya girgiza duniya, Yakan jijjiga ginshiƙan da duniya take zaune a kansu.


Sai duniya ta raurawa ta girgiza, Harsashin duwatsu suka jijjigu, suka girgiza Saboda Allah ya husata!


Mutane za su ɓuya a kogwannin duwatsu, ko su haƙa ramummuka a ƙasa, suna ƙoƙarin tserewa daga fushin Ubangiji, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa, sa'ad da ya zo domin ya girgiza duniya.


Zan sa sammai su yi rawar jiki, duniya kuwa za a girgiza ta a inda take, a wannan rana sa'ad da ni, Ubangiji Mai Runduna, na nuna fushina.


“Ga shi, kwanaki suna zuwa sa'ad da zan cika alkawarin da na yi wa mutanen Isra'ila da na Yahuza.


Gama a kishina da zafin hasalata na hurta, cewa a wannan rana za a yi babbar girgiza a ƙasar Isra'ila.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ