Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Haggai 2:2 - Littafi Mai Tsarki

2 “Ka yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukan sauran mutane, ka ce,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 “Ka yi magana da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel wanda yake gwamna a Yahuda, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da kuma dukan raguwar mutane. Ka tambaye su ka ce,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Haggai 2:2
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A rana ta fari ga watan shida a shekara ta biyu ta sarautar sarki Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Haggai, cewa ya yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.


Ubangiji kuwa ya zuga zuciyar Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da zuciyar Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da zuciyar dukan sauran mutane. Suka zo, suka fara aikin Haikalin Ubangiji Allahnsu Mai Runduna


Nehemiya kuwa wanda yake mai mulki, da Ezra, firist da magatakarda, da Lawiyawa waɗanda suka fassara wa jama'a dokokin, suka ce wa dukan jama'a, “Wannan rana tsattsarka ce, ta Ubangiji Allahnku, kada ku yi baƙin ciki ko kuka.” Gama mutane duka sai kuka suke sa'ad da aka karanta musu dokokin.


Sai mai mulki ya ce ba za su ci abinci mafi tsarki ba, sai firist ya shawarci Urim da Tummim tukuna, wato kamar kuri'a ke nan.


Sairus Sarkin Farisa ya sa ma'aji, Mitredat, ya fito da kayayyakin, ya ƙidaya wa Sheshbazzar, shugaban Yahuza.


Sai Yeshuwa ɗan Yehozadak tare da 'yan'uwansa, firistoci, da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel tare da 'yan'uwansu, suka tashi suka gina bagaden Allah na Isra'ila domin a miƙa hadayu na ƙonawa kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, mutumin Allah.


Zarubabel ɗan Sheyaltiyel kuwa, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukan sauran mutane, suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu, suka kuma yi biyayya da maganar annabi Haggai, kamar yadda Ubangiji Allahnsu ya faɗa masa. Mutane kuwa suka yi tsoron Ubangiji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ