Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Haggai 2:16 - Littafi Mai Tsarki

16 A lokacin, idan wani ya tafi wurin tsibin da zai auna mudu ashirin, sai ya iske mudu goma kawai. Idan kuma wani ya tafi wurin matse ruwan inabi don ya ɗebo mudu hamsin, sai ya tarar da mudu ashirin kawai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 A lokacin, idan wani ya tafi wurin tsibin da zai auna mudu ashirin, sai yă iske mudu goma kawai. Idan kuma wani ya tafi wurin matse ruwan inabi don yă ɗebo lita hamsin, sai yă tarar da lita ashirin kawai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Haggai 2:16
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kun yi shuka da yawa, kun girbe kaɗan. Kun ci, amma ba ku ƙoshi ba. Kun sha ruwa, amma bai kashe muku ƙishi ba. Kun sa tufafi, amma ba wanda ya ji ɗumi. Wanda yake karɓar albashi kuwa, sai ka ce yana sawa a huɗajjen aljihu.”


Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la'ana, zan la'antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la'antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Kadada biyar na gonar inabi za ta ba da kwalaba shida kaɗai na ruwan inabi. Garwa ashirin na iri za su ba da tsabar hatsi garwa biyu!”


An ɗauke farin ciki da murna daga ƙasa mai albarka ta Mowab, Na hana ruwan inabi malala daga wurin matsewarsa, Ba wanda yake matse shi, yana ihu na murna, Ihun da ake yi ba na murna ba ne.


“ ‘Ina roƙonku, ku tuna a ran nan tun kafin a ɗora dutse a kan dutse na gina Haikalin Ubangiji, yaya kuke?


Na aukar muku da burtuntuna, da fumfuna, da ƙanƙara a kan amfanin gonakinku, duk da haka ba ku komo wurina ba, ni Ubangiji na faɗa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ