Haggai 2:14 - Littafi Mai Tsarki14 Sai Haggai ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Haka yake da wannan jama'a da wannan al'umma da take gabana da kowane irin aikinsu. Abin da suke miƙawa kuma marar tsarki ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Sai annabi Haggai ya ce, “ ‘Haka yake da wannan mutane da kuma wannan al’umma a gabana,’ in ji Ubangiji. ‘Duk abin da suke yi da kuma dukan abin da suke miƙawa ƙazantattu ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu'a ga gumaka. Suna jin daɗin al'amuran banƙyama a lokacin yin sujada.