Gama ya kamata bakin firist ya kiyaye ilimi, wajibi ne firistoci su koyar da ilimin gaskiya na Allah, a gare su mutane za su tafi su koyi nufina, domin su manzannina ne, ni Ubangiji Mai Runduna.
mai riƙe da tabbatacciyar maganar nan kankan, daidai yadda aka koya masa, domin yă iya ƙarfafa wa waɗansu zuciya da sahihiyar koyarwa, ya kuma ƙaryata waɗanda suka yi musunta.
Firistocinta sun karya dokokina, sun ƙazantar da tsarkakan abubuwana. Ba su bambanta tsakanin abin da yake mai tsarki da marar tsarki ba, ba su kuma koyar da bambancin da yake tsakanin halal da haram ba. Ba su kiyaye ranar Asabar ɗina ba, da haka suke saɓon sunana.