Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Haggai 1:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Mutanen nan suna cewa lokaci bai yi ba tukuna da za a sāke gina Haikalin Ubangiji.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Waɗannan mutane sun ce, ‘Lokaci bai yi ba tukuna da za a gina gidan Ubangiji.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Haggai 1:2
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da aka karanta wa Rehum, da Shamshai magatakarda, da abokansu, wasiƙar sarki Artashate, suka hanzarta suka tafi wurin Yahudawa a Urushalima, suka gwada musu iko, suka tilasta musu su daina ginin.


Mutanen Yahuza kuwa suka ce, “Ƙarfin ma'aikata yana kāsawa, Akwai komatsai da yawa da za a kwashe, Yaya za mu iya gina garun yau?”


Wanda yake la'akari da iska, ba zai yi shuka ba, wanda kuma yake la'akari da gizagizai, ba zai yi girbi ba.


Duk abin da kake iya yi, ka yi shi da iyakar iyawarka, domin ba aiki, ko tunani, ko ilimi, ko hikima a lahira, gama can za ka.


Sai mutanen da suka tafi tare da shi suka amsa suka ce, “Ba za mu iya haurawa, mu kara da mutanen ba, gama sun fi mu ƙarfi.”


Jin tsoron mutane tarko ne, amma wanda ya dogara ga Ubangiji za a ɗaukaka shi.


Malalaci yakan yi zamansa a gida, yakan ce, “Zaki zai kama ni in na fita waje.”


A rana ta fari ga watan shida a shekara ta biyu ta sarautar sarki Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Haggai, cewa ya yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.


Ubangiji kuwa ya yi magana da annabi Haggai ya ce,


Saboda haka Yowash ya kirawo Yehoyada, firist, da sauran firistoci, ya ce musu, “Me ya sa ba ku gyara Haikalin? Daga yanzu kada ku karɓi kuɗi daga wurin abokanku, sai in za ku ba da shi domin gyaran Haikalin.”


Da lokacin kisa, da lokacin rayarwa, Da lokacin rushewa, da lokacin ginawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ