Sai suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Domin bayinka sun ji labari Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa ya ba ku ƙasar duka, ku hallaka dukan mazaunan ƙasar a gabanku, don haka muka ji tsoronku ƙwarai saboda rayukanmu, shi ya sa muka yi haka.
Gama mun ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Bahar Maliya ya ƙafe a gabanku a sa'ad da kuka fito daga Masar, da irin abin da kuka yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin Urdun, wato Sihon da Og, waɗanda kuka hallakar da su sarai.
Za a kwashe alfarwansu da garkunansu, Da labulan alfarwansu, da dukan kayansu. Za a kuma tafi da raƙumansu, Za a gaya musu cewa, ‘Razana ta kewaye ku!’
Da Fir'auna ya ji, sai ya nema ya kashe Musa. Amma Musa ya gudu daga gaban Fir'auna, ya tafi, ya zauna a ƙasar Madayana. Da ya kai, sai ya zauna a bakin wata rijiya.