15 Ka tattake teku da dawakanka, Da haukan ruwa mai ƙarfi.
15 Ka tattake teku da dawakanka, kana kaɗa manyan ruwaye.
Ka yi tafiya a teku, Ka haye teku mai zurfi, Amma ba a ga shaida inda ka taka ba.
Ya Ubangiji, ka hasala da koguna ne? Ko kuwa ka yi fushi da koguna? Ko kuwa ka hasala da teku ne, Sa'ad da ka hau dawakanka, kana bisa karusarka ta nasara?
Da hucin numfashin hancinka ruwa ya tattaru, Rigyawa ta tsaya kamar tudu, Zurfafan ruwa suka daskare a tsakiyar bahar.
Ka bi da jama'arka yadda makiyayi yake yi, Musa da Haruna suke lura da su.