Habakkuk 2:19 - Littafi Mai Tsarki19 Tasa ta ƙare, shi wanda ya ce da abin da aka yi da itace, ‘Farka!’ Ya kuma ce wa dutse wanda ba ya ji, ‘Tashi!’ Wannan zai iya koyarwa? Ga shi, an dalaye shi da zinariya da azurfa, Ba ya numfashi ko kaɗan. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202019 Kaito wanda ya ce da katako, ‘Rayu!’ Ko kuwa dutse marar rai, ‘Farka!’ Zai iya bishewa ne? An dalaye shi da zinariya da azurfa; ba numfashi a cikinsa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.