Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Habakkuk 2:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Ɓarnar da aka yi wa Lebanon za ta komo kanka, Ka kashe dabbobinta, yanzu dabbobi za su tsorata ka, Saboda jinin mutanen da ka zubar, Da wulakancin da ka yi wa duniya, Da birane, da mazauna a cikinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Ɓarnar da ka yi wa Lebanon zai komo kanka, kuma hallakar dabbobin da ka yi zai sa dabbobi su tsorata ka. Gama ka zub da jinin mutum; ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Habakkuk 2:17
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda ka washe al'umman duniya da yawa, Sauran mutanen duniya duka za su washe ka, Saboda jinin mutane, da wulakancin da ka yi wa duniya, Da birane, da mazauna a cikinsu.


Ki buɗe ƙofofinki, ke Lebanon, Don wuta ta cinye itatuwan al'ul naki.


Amma kai, ya Allah, za ka jefar da masu kisankai, da maƙaryata can ƙasa cikin zurfafa, Kafin su kai rabin kwanakinsu a duniya. Amma ni, zan dogara gare ka.


Ubangiji ya ce, “Zan sāka wa Babila da dukan mazaunan Kaldiya a ganin idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona.


Ku ji, sun gudu sun tsere daga ƙasar Babila, Don su faɗa cikin Sihiyona, Sakayyar Ubangiji Allahnmu domin Haikalinsa.


Mutumin da yake da laifin kisankai, yana haƙa wa kansa kabari da gaggawa. Kada ka yi ƙoƙarin hana shi.


Babila, za a hallaka ki! Mai farin ciki ne shi wanda ya sāka miki Bisa ga abin da kika yi mana.


“Dukanku 'yan baka, ku ja dāga, ku kewaye Babila, Ku harbe ta, kada ku rage kibanku, Gama ta yi wa Ubangiji zunubi.


A wurin yawan kasuwancinka, Ka yi rikici da yawa har ka yi zunubi. Don haka na jefar da kai daga dutsen Allah Kamar ƙazantaccen abu. Na hallaka ka daga tsakiyar duwatsu na wuta, Kai mala'ikan tsaro.


Al'ummai suka yi rawar jiki saboda amon faɗuwarsa, sa'ad da na jefar da shi cikin lahira tare da waɗanda suke gangarawa zuwa cikin kabari. Dukan itatuwan Aidan da itatuwa mafi kyau na Lebanon waɗanda suka ƙoshi da ruwa, sun ta'azantu a lahira.


“Masar za ta zama hamada, Edom kuma za ta zama kufai, Saboda kama-karya da suka yi wa mutanen Yahuza, Saboda sun zubar da jinin marasa laifi a ƙasarsu,


Za su ci gaba da juye tarunsa ke nan? Su yi ta karkashe al'umman duniya ba tausayi?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ