Habakkuk 1:16 - Littafi Mai Tsarki16 Domin haka sukan miƙa hadaya ga tarunsa, Su ƙona turare ga ragarsu, Domin su ne suka jawo musu wadata, da abinci mai yawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202016 Saboda haka yakan yi hadaya wa abin kamun kifinsa yă kuma ƙona turare wa ragarsa, domin ta wurin abin kamun kifinsa ne yake yin rayuwar jin daɗi yă kuma zaɓi irin abincin da yake so. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.