Muna kuma yi muku gargaɗi, 'yan'uwa, ku tsawata wa malalata, ku ƙarfafa masu rarraunar zuciya, ku taimaki marasa tsayayyiyar zuciya, ku yi haƙuri da kowa da kowa.
Shi kansa ya ɗauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume, domin mu yi zamanmu matattu ga zunubi, rayayyu kuma ga adalci. Da raunukansa ne aka warkar da ku.
Ga marasa Shari'a kuwa, sai na zama kamar marar Shari'a, ba cewa ba wata shari'ar Allah da take iko da ni ba, a'a, shari'ar Almasihu na iko da ni, domin in rinjayi marasa Shari'a ne.
Sai Yesu ya ce, “Ku kuma kaitonku, masanan Attaura! Don kuna jibga wa mutane kaya masu wuyar ɗauka, ku da kanku ko ɗan yatsa ba kwa sawa ku tallafa musu!
“To, ba irin wannan azumi ne na zaɓa ba? Wato ku kwance sarƙoƙin mugunta, ku kwance masu karkiya, ku 'yantar da waɗanda ake zalunta, ku kakkarye kowace karkiya.
Amma duk mai duba cikakkiyar ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake aikatawa.