8 Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne.
Na yi mamaki yadda nan da nan kuke ƙaurace wa wanda ya kira ku, bisa ga alherin Almasihu, har kuna koma wa wata baƙuwar bishara,
Mun kuma sani al'amura duka suna aikatawa tare, zuwa alheri ga waɗanda suke ƙaunar Allah, wato, waɗanda suke kirayayyu bisa ga nufinsa.
Waɗanda ya ƙaddarar nan kuwa, su ne ya kira. Waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar. Waɗanda ya kuɓutar ɗin kuwa, su ne ya ɗaukaka.