Ashe, ba ku sani ba, a wajen tsere dukan masu gudu suna ƙoƙarin tsere wa juna, amma ɗaya ne kaɗai yake samun kyautar ci? To, sai ku yi ta gudu haka nan, don ku ci.
Saboda haka, tun da taron shaidu masu ɗumbun yawa suka kewaye mu haka, sai mu ma mu yar da dukkan abin da ya nauyaya mana, da kuma zunubin da ya ɗafe mana, mu kuma yi tseren nan da yake gabanmu tare da jimiri,
Asirin nan kuwa sanar da shi ga dukan al'ummai, ta wurin littattafan annabawa, bisa ga umarnin Allah Madawwami, domin a jawo su, su gaskata, su yi biyayya.
Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka take yi, yawan masu bi kuma a birnin Urushalima sai ta ƙaruwa yake yi ƙwarai da gaske, firistoci masu yawan gaske kuma suka yi na'am da bangaskiyar nan.
Da umarnin wahayi ne na tafi, har na rattaba musu bisharar da nake yi a cikin al'ummai, amma a keɓance a gaban waɗansu shugabannin ikkilisiya, kada himmar da nake yi, ko wadda na riga na yi, ta zamana ta banza ce.