Haka kuma 'yan'uwana, kun zama matattu ga Shari'a, ta wurin jikin Almasihu, domin ku zama mallakar wani, wato, wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu ba da amfani ga Allah.
Sa'ad da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku cikin dukan gaskiya, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai faɗa, zai kuma sanar da ku al'amuran da za su auku.
yana kuma tunawa, cewa ita Shari'a ba a kafa ta domin masu adalci ba, sai dai kangararru, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai,