Idan kowanne daga cikin dukan zuriyarku ya kusaci tsarkakakkun abubuwa, waɗanda Isra'ilawa suka keɓe domina, lokacin da yake ƙazantacce, wannan mutum ba zai ƙara kasancewa a gabana ba, wannan kuwa zai zama har dukan lokatai masu zuwa. Ni ne Ubangiji.
“Za ku yi kwana bakwai kuna cin abinci marar yisti. A rana ta fari za ku fitar da yisti daga cikin gidajenku, gama duk wanda ya ci abin da aka sa wa yisti tun daga rana ta fari har zuwa ta bakwai za a fitar da shi daga cikin Isra'ila.
Maganar nan ta tashi saboda 'yan'uwan ƙaryar nan ne, da aka shigo da su a asirce, waɗanda suka saɗaɗo su yi ganganen 'yancinmu da muke da shi ta wurin Almasihu Yesu, don dai su sa mu bauta.
Amma Bitrus ya ce mata, “Ƙaƙa kuka gama baki ku gwada Ruhun Ubangiji? Kin ji tafiyar waɗanda suka binne mijinki, har sun iso bakin ƙofa ma, za su kuwa ɗauke ki, su fitar da ke.”
Saboda haka Isra'ilawa ba su iya tsayawa a gaban abokan gābansu ba, sun ba da baya ga abokan gābansu, gama sun zama haramtattu don hallakarwa. Daɗai, ba zan kasance tare da ku ba, sai dai kun kawar da haramtattun abubuwa da suke cikinku.