Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Galatiyawa 4:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Amma a yanzu da kuka san Allah, ko ma dai a ce Allah ya san ku, ta yaya za ku sāke komawa a kan raunanan al'adu marasa biyan bukata, har kuna neman komawa ga bautarsu?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma a ce Allah ya san ku, yaya kuke sāke komawa ga ƙa’idodin duniya marasa ƙarfi, abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu ne?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Galatiyawa 4:9
30 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

In kuwa wani na ƙaunar Allah, to, Allah ya san shi.


Ashe, rashin azancinku har ya kai ga haka? Da kuka fara da Ruhu, ashe, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa?


Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.


Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.


“Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.


In kuwa bayan da suka tsere wa ƙazantar duniyar albarkacin sanin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu, suka kuma sāke sarƙafewa a ciki, har aka rinjaye su, ƙarshen zamansu ya fi na fari lalacewa ke nan.


Ta wani hali an soke wani umarni ta dā saboda rauninsa da kuma rashin amfaninsa,


Duk da haka, ƙaƙƙarfan harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa cewa, “Ubangiji ya san nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yă yi nesa da aikata mugunta.”


da nufin cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhu mai ba da hikima da bayani ga sanin Allah,


Domin shi Allah wanda ya ce, “Haske yă ɓullo daga duhu ya haskaka,” shi ne ya haskaka zukatanmu domin a haskaka mutane su san ɗaukakarsa a fuskar Yesu Almasihu.


Gama yanzu kamar a madubi muke gani duhu duhu, a ranar nan kuwa za mu gani ido da ido. A yanzu sanina sama sama ne, a ranar nan kuwa zan fahimta sosai, kamar yadda aka fahimce ni sosai.


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan yi yadda ka ce, gama ka sami tagomashi a wurina, na san ka, na kuma san sunanka.”


Waɗanda Allah ya riga ya zaɓa tun tuni, su ne ya ƙaddara su ɗauki kamannin Ɗansa, domin shi Ɗan yă zama na farko a cikin 'yan'uwa masu yawa.


Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko.


Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bi na.


Ni ne Makiyayi mai kyau. Na san nawa, nawa kuma sun san ni,


Kowane abu Ubana ne ya mallakar mini. Ba kuwa wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban sai Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so ya bayyana wa.


Duniya za ta cika da sanin ɗaukakar Ubangiji, Kamar yadda ruwa ya cika teku.


Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji’ ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”


Idan ka yi za ka san abin da ake nufi da tsoron Ubangiji. Za ka yi nasara a kan koyon sanin Allah.


Waɗanda suka san ka za su amince da kai, ya Ubangiji, Ba za ka ƙyale duk wanda ya zo gare ka ba.


Gama Ubangiji yana lura da al'amuran adalai, Amma al'amuran mugaye za su watse.


sai ka kasa kunne ga addu'arsa. Ka ji daga Sama, wurin zamanka, ka amsa masa abin da ya roƙe ka, domin dukan mutanen duniya su san sunanka, su kuma yi tsoronka kamar jama'arka, Isra'ilawa, domin kuma su sani wannan Haikali da na gina wurin da za a yi maka sujada ne.


Ku farka daga magagi, ku kama aikin adalci, ku daina yin zunubi. Waɗansu kam, ba su da sanin Allah. Na faɗi wannan ne don ku kunyata.


Don in wani ya sa ku bauta, kukan jure masa, ko ya yi muku ƙwace, ko ya more ku, ko ya nuna muka isa, ko kuwa ya mare ku.


Haka yake a gare mu, wato sa'ad da muke kamar yara, a cikin ƙangin bautar al'adun duniya muke.


Sabon ruwan inabi, ai, sai sababbin salkuna.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ